1 Ifraimu tana kiwon iska,Tana ta bin iskar gabas dukan yini.Tana riɓaɓɓanya ƙarya da kamakarya.Tana ƙulla yarjejeniya da Assuriya,Tana kai mai a Masar.”
2 Ubangiji yana da magana game da mutanen Yahuza,Zai hukunta Isra'ila saboda hanyoyinta,Zai sāka mata gwargwadon ayyukanta.
3 A cikin mahaifa kakansu Yakubu ya kama diddigen ɗan'uwansa,Sa'ad da ya zama baligi ya yi kokawa da Allah.
4 Ya yi kokawa da mala'ika ya yi rinjaye.Ya yi kuka, ya roƙi albarka.Ya sadu da Allah a Betel,A can Allah ya yi magana da shi.