11 Idan akwai laifi a Gileyad,Hakika za su zama wofi.A Gilgal ana sadaka da bijimai,Bagadansu za su zama kamar tsibin duwatsuA gyaffan kunyoyin gona.”
12 Kakanmu Yakubu ya gudu zuwa ƙasar Aram,A can Isra'ila ya yi barantaka saboda mace,Saboda mace ya yi kiwon tumaki.
13 Ta wurin annabi Ubangiji ya fito da mutanen Isra'ila daga Masar,Ta wurin annabi kuma ya kiyaye su.
14 Mutanen Ifraimu sun yi muguwar tsokana mai ta da fushi,Domin haka Ubangiji zai ɗora musu hakkin jini a kansu,Zai saka musu cin mutuncin da suka yi.