6 “Don haka zan shinge hanyarta da ƙaya,Zan gina mata garu don kada ta sami hanyar fita.
7 Za ta bi samarinta, amma ba za ta tarar da su ba.Za ta neme su, amma ba za ta same su ba.Sa'an nan za ta ce, ‘Zan koma wurin mijina na fari,Gama zamana na dā ya fi na yanzu!’
8 “Amma ba ta sani ni nake ba ta hatsi, da ruwan inabi, da mai,Da azurfa, da zinariya da yawaWaɗanda suka bauta wa gunkin nan Ba'al da su ba.
9 Don haka zan hana mata hatsi a kakarsa,Da ruwan inabi a kakarsa, da kuma ulu da lilinWaɗanda suka zama abin rufe tsiraicinta.
10 Yanzu zan buɗe tsiraicintaA idon samarinta,Ba kuwa wanda zai cece ta daga hannuna.
11 Zan sa ta daina farin cikinta,Da idodinta, da kiyaye lokatan amaryar wata,Da hutawar ranar Asabar,Da ƙayyadaddun idodinta.
12 Zan ɓata inabinta da itatuwan ɓaureWaɗanda take cewa, ‘Waɗannan su ne hakkinaWanda samarina suka ba ni.’Zan sa su zama kurmi,Namomin jeji su cinye su.