6 Mutanena sun lalace saboda jahilci.Tun da yake sun ƙi ilimi,Ni ma na ƙi ku da zaman firist ɗina.Tun da yake kun manta da umarnan Allahnka,Ni ma zan manta da 'ya'yanku.
7 “Yawan ƙaruwar firistoci, yawan ƙaruwar zunubi.Zan sāke darajarsu ta zama kunya.
8 Suna ciyar da kansu da zunubin mutanena,Suna haɗamar ribar muguntarsu.
9 Kamar yadda mutane suke, haka firistocin suke,Zan hukunta su saboda al'amuransu,Zan sāka musu gwargwadon ayyukansu.
10 Za su ci, amma ba za su ƙoshi ba.Za su yi karuwanci, amma ba za su ƙaru ba.Gama sun rabu da Ubangiji don su bauta wa gumaka.
11 “Karuwanci, da ruwan inabi,Da ruwan inabin da bai sa hauka ba sukan kawar da hankali.
12 Mutanena sukan yi tambaya a wurin abin da aka yi da itace,Sandansu yakan faɗa musu gaiɓu,Gama ruhun karuwanci ya ɓad da su,Sun rabu da Allahnsu don su yi karuwanci.