2 Sun tayar, sun yi zurfi cikin zunubi,Zan hore su duka.
3 Na san Ifraimu, Isra'ila kuma ba a ɓoye take a gare ni ba.Gama Ifraimu ta yi aikin karuwanci,Isra'ila kuma ta ƙazantu.
4 “Ayyukansu ba su bar suSu koma wurin Allahnsu ba,Gama halin karuwanci yana cikinsu,Don haka kuma ba su san Ubangiji ba.
5 Girmankan mutanen Isra'ila yana ba da shaida a kansu.Mutanen Ifraimu za su yi tuntuɓe cikin laifinsu.Mutanen Yahuza kuma za su yi tuntuɓe tare da su.
6 Da garkunan tumaki da na awaki, da na shanunsuZa su tafi neman Ubangiji,Amma ba za su same shi ba,Gama ya rabu da su.
7 Sun ci amanar Ubangiji.Su haifi shegu.Yanzu amaryar wata za ta cinye su da gonakinsu.
8 “Ku busa ƙaho cikin Gibeya,Ku busa kakaki cikin Rama,Ku yi gangami cikin Bet-awen,Ku yi rawar yaƙi, ya ku Biliyaminu!