2 Bayan kwana biyu zai rayar da mu.A rana ta uku kuwa zai tashe muMu yi zammanmu a gabansa.
3 Mu nace domin mu san UbangijiZuwansa tabbatacce ne kamar wayewar gari.Zai zo wurinmu kamar ruwan sama,Kamar ruwan bazara da yake shayar da ƙasa.”
4 Ubangiji ya ce, “Me zan yi da ke, ya Ifraimu?Me zan yi da ke, ya Yahuza?Ƙaunarku tana kama da ƙāsashi,Kamar kuma raɓar da take watsewa da wuri.
5 Domin haka na sassare su ta wurin annabawansu,Na karkashe su da maganar bakina.Hukuntaina suna kama da hasken da yake ketowa.
6 Gama ƙauna nake so, ba sadaka ba,Sanin Allah kuma fiye da hadayu na ƙonawa.
7 “Amma sun ta da alkawarina kamar Adamu,Sun ci amanata.
8 Gileyad gari ne na masu aikata mugunta.Tana da tabban jini.