7 “Amma sun ta da alkawarina kamar Adamu,Sun ci amanata.
8 Gileyad gari ne na masu aikata mugunta.Tana da tabban jini.
9 Kamar yadda mafasa sukan yi fakon mutum,Haka nan firistoci suka haɗa kansuDon su yi kisankai a hanyar Shekem,Ai, sun aikata mugayen abubuwa.
10 Na ga abin banƙyama a cikin Isra'ila,Karuwancin Ifraimu yana wurin,Isra'ila ta ƙazantar da kanta.
11 “Ku kuma, ya mutanen Yahuza, an shirya muku ranar girbi,A lokacin da zan mayar wa mutanena da dukiyarsu.”