1 “Sa'ad da zan warkar da mutanen Isra'ila,Sai zunubin Ifraimu da muguntar Samariya su bayyana,Gama suna cin amana.Ɓarawo yakan fasa, ya shiga,'Yan fashi suna fashi a fili,
2 Amma ba su tunani,Cewa zan tuna da dukan muguntarsu.Yanzu ayyukansu sun kewaye su,Ina ganinsu.
3 “Suna faranta zuciyar sarki da muguntarsu,Na shugabanni kuma da ƙarairayinsu.
4 Dukansu mazinata ne,Suna kama da tanda da aka zafafa,Wadda matoyi ya daina iza mata wuta,Tun daga lokacin cuɗe kulluHar zuwa lokacin da yisti ya tasar da shi.
5 A ranar bikin sarki,Sukan sa sarki da shugabanni su bugu da ruwan inabi.Yakan yi cuɗanya da shakiyai.
6 Zukatansu suna ƙuna da ƙullaƙulle kamar tanderu.Fushinsu na ci dare farai,Da safe fushinsu yana ci bal-bal kamar harshen wuta.