2 Amma ba su tunani,Cewa zan tuna da dukan muguntarsu.Yanzu ayyukansu sun kewaye su,Ina ganinsu.
3 “Suna faranta zuciyar sarki da muguntarsu,Na shugabanni kuma da ƙarairayinsu.
4 Dukansu mazinata ne,Suna kama da tanda da aka zafafa,Wadda matoyi ya daina iza mata wuta,Tun daga lokacin cuɗe kulluHar zuwa lokacin da yisti ya tasar da shi.
5 A ranar bikin sarki,Sukan sa sarki da shugabanni su bugu da ruwan inabi.Yakan yi cuɗanya da shakiyai.
6 Zukatansu suna ƙuna da ƙullaƙulle kamar tanderu.Fushinsu na ci dare farai,Da safe fushinsu yana ci bal-bal kamar harshen wuta.
7 “Dukansu suna da zafi kamar tanderu.Suna kashe masu mulkinsu.Dukan sarakunansu sun faɗi.Ba wanda ya kawo mini kuka.”
8 Ubangiji ya ce, “Mutanen Ifraimu sun haɗa kansu da al'ummai,Sun zama kamar wainar da ba a juya ba.