1 Ubangiji ya ce, “Ki sa ƙaho a bakinki,Kamar gaggafa, haka maƙiyi ya kawo sura a kan ƙasar Ubangiji,Domin mutanena sun ta da alkawarina,Sun kuma keta dokokina.
2 Sun yi kuka a wurina,Suna cewa, ‘Ya Allah, mu Isra'ila mun san ka!’
3 Isra'ila ta ƙi abin da yake mai kyau,Don haka abokan gāba sun fafare ta.
4 “Suna naɗa sarakuna, amma ba da iznina ba.Suna naɗa shugabanni amma ba da yardata ba.Suna ƙera gumaka da azurfarsu da zinariyarsu,Wannan kuwa zai zama sanadin halakarsu.
5 Ya mutanen Samariya, ina ƙin maraƙinku na siffa.Ina jin haushinsu ƙwarai!Sai yaushe za su rabu da gumaka?