7 Gama sun shuka iskaDon haka zu su girbe guguwa.Hatsin da yake tsaye ba shi da zangarniya,Ba zai yi tsaba ba.Ko da ya yi tsaba ma, baƙi ne za su ci,
8 Isra'ila kamar kowace al'umma ce.Suna cikin al'ummaiKamar kaskon da ba shi da amfani,
9 Gama sun haura zuwa Assuriya,Kamar jakin jeji da yake yawo shi kaɗai.Mutanen Ifraimu sun yi ijara da abokan tsafinsu.
10 Ko da yake sun yi ijara da abokai daga cikin al'ummai,Yanzu zan tattara su, in hukunta su.Sa'an nan za su fara ragowa,Ta wurin tunanin nawayar Sarkin sarakuna.
11 “Da yake Ilfraimu ta yawaita bagadan zunubi,Sun zama mata bagadai na yin zunubi.
12 Ko da na rubuta mata dokokina sau da yawo,Za ta ɗauke su wani baƙon abu ne kawai.
13 Suna jin daɗin miƙa hadayu don cin naman,Amma Ubangiji ba ya jin daɗinsu.Ubangiji zai tuna da muguntarsu,Zai hukunta su saboda zunubansu.Za su koma Masar.