10 “Zan cika zuriyar Dawuda da mutanen Urushalima da ruhun tausayi da na addu'a. Za su dubi wanda suka soke shi, har ya mutu. Za su yi makoki dominsa kamar waɗanda aka yi musu rasuwar ɗan farinsu.
11 A ran nan za a yi babban makoki a Urushalima kamar mutane suka yi wa Hadadrimmon a filin Magiddo.
12 Kowane iyali a ƙasar za su yi makokinsu a keɓe, iyalin gidan Dawuda kuma za su yi nasu a keɓe, matansu za su yi nasu a keɓe. Iyalin gidan Natan su ma za su yi nasu makoki a keɓe, matansu kuma a keɓe.
13 Iyalin gidan Lawi za su yi makokinsu a keɓe, matansu kuma a keɓe. Iyalin gidan mutanen Shimai za su yi makokinsu a keɓe, matansu kuma a keɓe.
14 Sauran dukan iyalan da suka ragu za su yi nasu makoki a keɓe, matansu kuma a keɓe.”