8 Zan kafa sansani kewaye da Haikalina saboda maƙiya,Don masu kai da kawowa.Ba wani azzalumi da zai ci su da yaƙi,Gama yanzu ni kaina na gani.”
9 Ki yi murna ƙwarai, ya Sihiyona!Ta da murya ya Urushalima!Ga Sarkinki yana zuwa wurinki,Shi mai adalci ne, mai nasara,Shi kuma mai tawali'u ne,Yana bisa kan jaki, a kan aholaki.
10 Ubangiji ya ce,“Zan datse karusa daga Ifraimu,In datse ingarman yaƙi a Urushalima,Zan kuma karya bakan yaƙi.Sarkinki zai tabbatar wa al'umman duniya da salama,Mulkinsa zai zama daga teku zuwa teku,Daga Kogin Yufiretis zuwa matuƙar duniya.”
11 Ubangiji ya ce,“Ke kuma, saboda jinin alkawarina da yake tsakanina da ke,Zan 'yantar da waɗanda suke cikin rami,Waɗanda aka kama daga cikinki.
12 Ku koma mafakarku, ku ɗaurarru masu sa zuciya.Gama yanzu zan sāka muku har ninki biyu.
13 Gama na tankwasa Yahuza ta zama bakana,Na kuma mai da Ifraimu ta zama kibiya,Zan yi amfani da mutanen Sihiyona kamar takobi,Su yi yaƙi da mutanen Hellas.”
14 Ubangiji kuwa zai bayyana kansa gare su,Kibiyarsa za ta fita kamar walƙiya,Ubangiji Allah zai busa ƙaho,Zai taho ta cikin guguwa daga kudu.