20 A'a! Na nuna ne kawai cewa abin da al'ummai suke yankawa, ga aljannu suke yanka wa, ba Allah ba. Ba na fa so ku zama abokan tarayya da aljannu.
21 Ba dama ku sha a ƙoƙon Ubangiji, ku kuma sha a na aljannu. Ba dama ku ci abinci a teburin Ubangiji, ku kuma ci a na aljannu.
22 Ashe, har mā tsokani Ubangiji ya yi kishi? Mun fi shi ƙarfi ne?
23 “Dukan abubuwa halal ne,” amma ba dukan abubuwa ne masu amfani ba. “Dukan abubuwa halal ne,” amma ba dukan abubuwa ne suke ingantawa ba.
24 Kada kowa ya nemi ya kyautata wa kansa, sai dai ya kyautata wa ɗan'uwansa.
25 Ku ci kowane irin abu da ake sayarwa a mahauta, ba tare da tambaya ba saboda lamiri.
26 Don an rubuta, “Duniya ta Ubangiji ce, da duk abin da yake cikinta.”