25 Haka kuma bayan jibin, sai ya ɗauki ƙoƙo, ya ce, “Ƙoƙon nan na Sabon Alkawari ne, da aka tabbatar da shi da jinina. Ku yi haka duk a sa'ad da kuke sha, domin tunawa da ni.”
26 Wato, duk sa'ad da kuke cin gurasar nan, kuke kuma sha a ƙoƙon nan, kuma ayyana mutuwar Ubangiji ke nan, har sai ya dawo.
27 Saboda haka duk wanda ya ci gurasar nan, ko ya sha a ƙoƙon nan na Ubangiji da rashin cancanta, ya yi laifin wulakanta jikin Ubangiji da jininsa ke nan.
28 Sai dai kowa ya auna kansa, sa'an nan ya ci gurasar, ya kuma sha a ƙoƙon.
29 Kowa ya ci, ya kuma sha, ba tare da faɗaka da jikin Ubangiji ba, ya jawo wa kansa hukunci ke nan, ta wurin ci da sha da ya yi.
30 Shi ya sa da yawa daga cikinku suke da rashin lafiya da rashin ƙarfi, har ma waɗansu da dama suka yi barci.
31 Amma in da za mu auna kanmu sosai, da ba za a hukunta mu ba.