3 Amma fa ina so ku fahimci cewa, shugaban kowane mutum Almasihu ne, shugaban kowace mace kuwa mijinta ne, shugaban Almasihu kuma Allah ne.
4 Duk mutumin da ya yi addu'a ko ya yi annabci kansa a rufe, ya wulakanta shugabansa ke nan.
5 Amma duk matar da ta yi addu'a, ko ta yi annabci da kanta a buɗe, ta wulakanta shugabanta ke nan, duk ɗaya ne da an aske kanta ma.
6 In mace ta ƙi rufe kanta, to, sai ta sausaye gashinta. In kuwa abin kunya ne a yi wa mace sausaye ko kundumi, to, sai ta rufe kanta.
7 Namiji kam, bai kamata yă rufe kansa ba, tun da yake shi kamannin Allah ne, abin alfahari ga Allah kuma. Amma mace abar taƙamar namiji ce.
8 (Don kuwa namiji ba daga jikin mace yake ba, amma matar daga jikin namiji take.
9 Ba a kuma halicci namiji don mace ba, sai dai mace don namiji.)