2 To, lalle ne mai kula da ikkilisiya yă zama marar abin zargi, yă zama mai mace ɗaya, mai kamunkai, natsattse, kintsattse, mai yi wa baƙi alheri, gwanin koyarwa kuma.
3 Ba mashayi ba, ba mai saurin dūka ba, amma salihi, ba kuma mai husuma ba, ba kuwa mai son kuɗi ba.
4 Lalle ne yă iya sarrafa iyalinsa da kyau, yana kuma kula da 'ya'yansa, su yi biyayya da matuƙar ladabi.
5 Don kuwa in mutum bai san yadda zai sarrafa iyalinsa ba, ta ƙaƙa zai iya kula da ikkilisiyar Allah?
6 Lalle ne kuma, kada yă zama sabon tuba, don kada yă daga kai yă burmu a cikin hukuncin da aka yi wa Iblis.
7 Banda haka kuma, lalle ne yă zama mai mutunci ga waɗanda ba su a cikinmu, don kada yă zama abin zargi, yă faɗa a cikin tarkon Iblis.
8 Haka kuma masu hidimar ikkilisiya, lalle ne su zama natsattsu, ba masu baki biyu ba, ko mashaya, ko masu kwaɗayin ƙazamar riba.