4 Domin duk abin da Allah ya halitta kyakkyawa ne, kada kuma a ƙi kome muddin an karɓe shi da godiya,
5 gama an tsarkake shi ta wurin Maganar Allah da addu'a
6 In kana tuna wa 'yan'uwa wadannan abubuwa, za ka zama amintaccen bawan Almasihu Yesu, wanda aka goya da maganar bangaskiya, da kuma sahihiyar koyarwar nan wadda ka bi har ya zuwa yau.
7 Ka ƙi tatsuniyoyin saɓo da na banza da wofi. Ka hori kanka ga bin Allah.
8 Horon jiki yana da ɗan amfaninsa, amma bin Allah yana da amfani ta kowace hanya, da yake shi ne da alkawarin rai na a yanzu da na nan gaba.
9 Maganar nan tabbatacciya ce, ta kuma cancanci a karɓe ta ɗungum.
10 Saboda wannan maƙasudi muke wahala, muke ta fama, domin mun dogara ne ga Allah Rayayye, wanda yake Mai Ceton dukan mutane, musamman masu ba da gaskiya.