2 Ya ku ƙaunatattuna, a yanzu mu 'ya'yan Allah ne, yadda za mu zama nan gaba kuwa, ba a bayyana ba tukuna, amma mun sani sa'ad da ya bayyana, za mu zama kamarsa, domin za mu gan shi kamar yadda yake.
3 Duk mai ƙwallafa sa zuciya gare shi haka, yana tsarkake kansa ke nan, kamar yadda shi yake Mai Tsarki.
4 Duk mai aikata zunubi ya yi tawaye ke nan. Zunubi tawaye ne.
5 Kun dai sani an bayyana shi domin yă ɗauke zunubai ne, a gare shi kuma ba zunubi.
6 Kowa da yake a zaune a cikinsa, ba ya aikata zunubi. Kowa da yake aikata zunubi, bai taɓa ganinsa ba, bai ma san shi ba.
7 Ya ku 'ya'yana ƙanana, kada fa kowa ya ɓad da ku. Shi wanda yake aikata adalci, mai adalci ne, kamar yadda Almasihu mai adalci ne.
8 Duk mai aikata zunubi, na Iblis ne, don tun farko Iblis mai aikata zunubi ne. Dalilin bayyanar Ɗan Allah shi ne domin yă rushe aikin Iblis.