7 Ashe, laifi na yi da na ƙasƙantar da kaina, don a ɗaukaka ku, wato, saboda na yi muku bisharar Allah a kyauta?
8 Waɗansu ikilisiyoyi na biyan hakkina, sai ka ce ina yi musu ƙwace domin in yi muku hidima.
9 Sa'ad da nake a wurinku kuma nake zaman rashi, ban nauyaya wa kowa ba, domin 'yan'uwan da suka zo daga Makidoniya su ne suka biya mini bukata. Saboda haka, na ƙi nauyaya muku ta kowace hanya, ba kuwa zan nauyaya muku ba.
10 Albarkacin gaskiyar Almasihu da yake tare da ni, ba mai hana ni fahariyar nan tawa a lardin Akaya.
11 To, don me? Domin ba na ƙaunarku ne? Allah dai ya sani ina ƙaunarku.
12 Abin da nake yi kuwa, shi zan riƙa yi, domin in toshe kafar mutanen nan da suke fariya, suna nema mu daidaita da su.
13 Irin waɗannan mutane manzannin ƙarya ne, mayaudaran ma'aikata, suna mai da kansu kamar su manzannin Almasihu ne.