12 An gudanar da tabbatattun alamun manzo a cikinku ta matuƙar jimiri, da alamu da abubuwan al'ajabi da mu'ujizai.
13 Ta wace hanya ce kuka kasa sauran ikkilisiyoyi? Ko kuwa domin dai ni ban nauyaya muku ba? To, ku yafe mini wannan laifi!
14 Ga shi, na yi shirin zuwa wurinku, zuwa na uku, ba kuwa zan nauyaya muku ba, don ba abinku nake nema ba, ku nake nema, domin ba yara ne da ɗaukar nauyin iyayensu ba, sai dai iyaye ne da ɗaukar nauyin yaran.
15 Ni kam, zan kashe dukan abin hannuna da dukan zarafina da matuƙar farin ciki saboda ranku. In na ƙara ƙaunarku, ashe, sai a rage ƙaunata?
16 To, a ce ban nauyaya muku ba ɗin, ashe, sai ku ce dabara na yi muku, na shawo kanku ta hanyar yaudara!
17 Na cuce ku ne ta wurin wani daga cikin waɗanda na aiko a gare ku?
18 Na roƙi Titus ya je, na kuma aiko ɗan'uwan nan tare da shi. To, Titus ya cuce ku ne? Ashe, ba Ruhu ɗaya yake bi da mu ba, ni da shi? Ba kuma hanya ɗaya muke bi ba?