2 Ba ruwanmu da ɓoye-ɓoye na munafunci, ko makirci, ko yi wa Maganar Allah algus, amma ta wurin bayyana gaskiya a fili, sai kowane mutum ya shaidi gaskiyarmu a lamirinsa a gaban Allah.
3 Ko da bishararmu a rufe take, ai, ga waɗanda suke hanyar hallaka kaɗai take a rufe.
4 Su ne marasa ba da gaskiya, waɗanda sarkin zamanin nan ya makantar da hankalinsu, don kada hasken bisharar ɗaukakar Almasihu, shi da yake surar Allah, ya haskaka su.
5 Domin ba wa'azin kanmu muke yi ba, sai dai na Yesu Almasihu a kan shi ne Ubangiji, mu kuwa bayinku ne saboda Yesu.
6 Domin shi Allah wanda ya ce, “Haske yă ɓullo daga duhu ya haskaka,” shi ne ya haskaka zukatanmu domin a haskaka mutane su san ɗaukakarsa a fuskar Yesu Almasihu.
7 Wannan wadata da muke da ita kuwa, a cikin kasake take, wato, jikunanmu, don a nuna mafificin ikon nan na Allah ne, ba namu ba.
8 Ana wahalshe mu ta kowace hanya, duk da haka, ba a ci ɗunguminmu ba. Ana ruɗa mu, duk da haka ba mu karai ba.