5 har ma suka bayar fiye da yadda muka zata, amma sai da suka fara miƙa kansu ga Ubangiji da a gare mu kuma, bisa ga nufin Allah.
6 Ganin haka sai muka roƙi Titus, da yake shi ne ya riga ya tsiro da wannan aikin alheri a cikinku, sai yă ƙarasa shi.
7 To, da yake kun fifita a kowane abu, wato, a cikin bangaskiya, da magana, da sani, da matuƙar himma, da kuma ƙaunar da kuke yi mana, to, sai ku fifita a wannan aikin alheri ma.
8 Ba kallafa muku wannan nake yi ba, sai dai ta nuna himmar waɗansu, in tabbata ƙaunarku ma sahihiya ce.
9 Domin kun san alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu, ko da yake shi mawadaci ne, sai ya zama matalauci sabili da ku, domin ta wurin talaucinsa ku wadata.
10 A wannan al'amari, ga shawarata. Ai, ya fiye muku a yanzu ku ƙarasa abin da kuka fara yi a bara, har kuka yi da ra'inku.
11 To, sai ku ƙarasa aikin da irin ra'in da kuka fara, gwargwadon ikonku.