11 Za a wadata ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa a yalwace, bayarwar nan kuwa da za ku yi, za ta zama sanadin godiya ga Allah ta wurinmu.
12 Domin aikin nan na alheri, ba biyan bukatar tsarkaka kaɗai yake yi ba, har ma yana ƙara yawaita godiya ga Allah ƙwarai da gaske.
13 Aikin nan naku na alheri tabbatar bangaskiyarku ne, za a kuwa ɗaukaka Allah saboda kun bayyana yarda, cewa kun yi na'am da bisharar Almasihu, saboda kuma gudunmawa da kuka yi musu da saura duka, hannu sake.
14 Su kuwa za su yi muku addu'a, su yi ɗokin ganinku saboda alherin Allah marar misaltuwa da ya yi muku.
15 Godiya tā tabbata ga Allah saboda baiwarsa da ta fi gaban a faɗa.