24 Bayan 'yan kwanaki Filikus ya zo tare da matarsa, Durusila, wata Bayahudiya. Sai ya aika a zo da Bulus, ya kuwa saurare shi a kan maganar gaskatawa da Almasihu Yesu.
25 Bulus yana ba da bayani a kan adalci, da kamunkai, da kuma hukuncin nan mai zuwa, Filikus ya kaɗu, ya kāda baki ya ce, “Yanzu kam, sai ka koma. In na sami zarafi nā kira ka.”
26 Don yana sa rai Bulus zai ba shi kuɗi, shi ya sa ya yi ta kiransa a kai a kai, yana zance da shi.
27 Amma bayan shekara biyu sai Borkiyas Festas ya gāji Filikus. Filikus kuwa don neman farin jini a wurin Yahudawa, ya bar Bulus a ɗaure.