4 domin in bayyana shi sosai, kamar yadda ya kamata in faɗa.
5 Ku tafiyar da al'amuranku da hikima a cikin zamanku tare da marasa bi, kuna matuƙar amfani da lokaci.
6 A kullum maganarku ta zama mai ƙayatarwa, mai daɗin ji, domin ku san irin amsar da ta dace ku ba kowa.
7 Tikikus zai sanar da ku duk abin da nake ciki. Shi ƙaunataccen ɗan'uwa ne, amintaccen mai hidima, abokin bautarmu kuma a cikin Ubangiji.
8 Na aiko shi a gare ku musamman, domin ku san yadda muke, yă kuma ƙarfafa muku zuciya.
9 Ga kuma Unisimas a nan tare da shi, amintaccen ɗan'uwa ƙaunatacce, wanda shi ma a cikinku yake. Su za su gaya muku duk abin da ya faru a nan.
10 Aristarkus, abokin ɗaurina, yana gaishe ku, haka kuma Markus, wanda kakansu ɗaya ne da Barnaba. Shi ne aka riga aka yi muku umarni a game da shi. In dai ya zo wurinku, ku karɓe shi.