37 Ba wata faɗar Allah da za ta kasa cika.”
38 Sai Maryamu ta ce, “To, ga shi, ni baiwar Ubangiji ce, yă zama mini yadda ka faɗa.” Sai mala'ikan ya tashi daga gare ta.
39 A kwanakin nan Maryamu ta tashi da hanzari, ta tafi wata ƙasa mai duwatsu, zuwa wani gari na ƙasar Yahuza.
40 Ta shiga gidan Zakariya ta gai da Alisabatu.
41 Sai ya zamana da Alisabatu ta ji gaisuwar Maryamu, jariri ya motsa da ƙarfi a cikinta. Aka kuwa cika Alisabatu da Ruhu Mai Tsarki,
42 har ta tā da murya da ƙarfi, ta ce, “Ke mai albarka ce a cikin mata, ɗan cikinki kuma mai albarka ne!
43 Ta yaya wannan alheri ya same ni, har da uwar Ubangijina za ta zo gare ni?