7 Kai! ko da gashin kanku ma duk a ƙidaye yake. Kada ku ji tsoro. Ai, martabarku ta fi ta gwara masu yawa.”
8 “Ina kuma gaya muku, kowa ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, Ɗan Mutum ma zai bayyana yarda a gare shi a gaban mala'ikun Allah.
9 Wanda kuwa ya yi musun sanina a gaban mutane, za a yi musun saninsa a gaban mala'ikun Allah.
10 Kowa ya kushe wa Ɗan Mutum, ā gafarta masa, amma wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba.
11 Sa'ad da suka kai ku gaban majami'u, da mahukunta da shugabanni, kada ku damu da yadda za ku mai da jawabi, ko kuwa abin da za ku faɗa,
12 domin Ruhu Mai Tsarki zai koya muku abin da ya kamata ku faɗa a lokacin.”
13 Sai wani a cikin taron ya ce masa, “Malam, kă ce wa ɗan'uwana ya raba gādo da ni.”