16 Ashe, bai kamata matar nan 'yar zuriyar Ibrahim, wadda Shaiɗan ya ɗaure, yau shekara goma sha takwas, a kwance ta daga wannan ƙuƙumi a ran Asabar ba?”
17 Da ya faɗi haka, sai duk abokan adawarsa suka kunyata, duk taron kuwa suka yi ta farin ciki da abubuwan al'ajabi da yake yi.
18 Sai Yesu ya ce, “Da me Mulkin Allah yake kama? Da me kuma zan kwatanta shi?
19 Kamar ƙwayar mastad yake, wadda wani mutum ya je ya shuka a lambunsa, ta kuma girma ta zama itace, har tsuntsaye suka yi sheƙarsu a rassanta.”
20 Ya sāke cewa, “Da me zan kwatanta Mulkin Allah?
21 Kamar yisti yake wanda wata mace ta ɗauka ta cuɗa da mudu uku na garin alkama, har duk garin ya gama da yistin.”
22 Sai ya ɗauki hanyarsa ta zuwa birane da ƙauyuka, yana koyarwa, yana dosar Urushalima.