8 Sai ya amsa masa ya ce, ‘Ubangijina, bar shi dai bana ma, in yi masa kaftu, in zuba masa taki.
9 In ya yi 'ya'ya, to, in kuwa bai yi ba, sai a sare.’ ”
10 Wata rana yana koyarwa a wata majami'a ran Asabar,
11 sai ga wata mace wadda inna ta shanye tun shekara goma sha takwas, duk ta tanƙware, ko kaɗan ba ta iya miƙewa.
12 Da Yesu ya gan ta, sai ya kira ta ya ce mata, “Uwargida, an raba ki da rashin lafiyarki!”
13 Sai ya ɗora mata hannu, nan take ta miƙe, ta kuma ɗaukaka Allah.
14 Amma shugaban majami'a ya ji haushi, don Yesu ya warkar ran Asabar. Sai ya ce wa jama'a, “Akwai ranaku har shida da ya kamata a yi aiki. Ku zo mana a ranakun nan a warkar da ku, ba ran Asabar ba.”