3 Kowa sai ya tafi garinsu a rubuta shi.
4 Yusufu shi ma ya tashi daga birnin Nazarat, a ƙasar Galili, ya tafi ƙasar Yahudiya, ya je birnin Dawuda, da ake kira Baitalami (domin shi daga gidan Dawuda ne, na cikin zuriyarsa),
5 don a rubuta shi, duk da Maryamu tashinsa, wadda take kuma da ciki.
6 Sa'ad da suke can kuwa, sai lokacin haihuwarta ya yi.
7 Sai ta haifi ɗanta na fari, ta rufi shi da zanen goyo, ta kuma kwantar da shi a wani komi dabbobi, don ba su sami ɗaki a masaukin ba.
8 A wannan yankin ƙasa kuwa waɗansu makiyaya suna kwana a filin Allah, suna tsaron garken tumakinsu da dad dare.
9 Sai ga wani mala'ikan Ubangiji tsaye kusa da su, ɗaukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewayensu, har suka tsorata gaya,