6 Da Bilatus ya ji haka, ya tambaya ko mutumin nan Bagalile ne.
7 Da ya ji Yesu a ƙarƙashin mulkin Hirudus yake, sai ya aika da shi wurin Hirudus, don shi ma yana Urushalima a lokacin.
8 Da Hirudus ya ga Yesu, ya yi murna ƙwarai, saboda tun da daɗewa yake son ganinsa, don ya riga ya ji labarinsa, yana kuma fata ya ga wata mu'ujiza da Yesu zai yi.
9 Sai ya yi ta masa tambayoyi da yawa, amma bai amsa masa da kome ba.
10 Manyan firistoci da malaman Attaura na nan a tsaitsaye, suna tsananta kai ƙararrakinsa ainun.
11 Sai Hirudus da sojansa suka wulakanta shi, suka yi masa ba'a, da suka sa masa tufafi masu ƙawa kuma, suka mai da shi wurin Bilatus.
12 A ran nan sai Hirudus da Bilatus suka yi sulhu, don dā abokan gāba ne.