12 Haka fa, suka fita, suna wa'azi mutane su tuba.
13 Suka fitar da aljannu da yawa, suka kuma shafa wa marasa lafiya da yawa mai, suka warkar da su.
14 Sai fa sarki Hirudus ya ji labari, domin sunan Yesu ya riga ya shahara, har waɗansu suka ce, “Yahaya Maibaftisma ne aka tasa daga matattu, shi ya sa mu'ujizan nan suke aiki ta wurinsa.”
15 Amma waɗansu kuwa suka ce, “Iliya ne.” Waɗansu kuwa suka ce, “Ai, annabi ne, kamar ɗaya daga cikin annabawa.”
16 Amma da Hirudus ya ji haka, sai ya ce, “Yahaya, wanda na fille wa kai, shi ne aka tasa.”
17 Don dā Hirudus da kansa ya aika aka kamo Yahaya, ya ɗaure shi a kurkuku saboda Hirudiya matar ɗan'uwansa Filibus, wadda shi Hirudus ya aura.
18 Don dā Yahaya ya ce wa Hirudus, “Bai halatta ka zauna da matar ɗan'uwanka ba.”