24 Sa'an nan kuwa jirgin yana tsakiyar teku, raƙuman ruwa mangara tasa, gama iska tana gāba da su.
25 Wajen ƙarfe uku na dare sai Yesu ya nufo su, yana tafe a kan ruwan tekun.
26 Sa'ad da kuwa almajiran suka gan shi yana tafiya a kan ruwan, sai suka firgita suka ce, “Fatalwa ce!” Suka yi kururuwa don tsoro.
27 Sai nan da nan ya yi musu magana ya ce, “Ba kome, Ni ne, kada ku ji tsoro.”
28 Sai Bitrus ya amsa ya ce, “Ya Ubangiji, in kai ne, to, ka umarce ni in zo gare ka a kan ruwan.”
29 Ya ce, “Zo mana.” Sai Bitrus ya fita daga jirgin, ya taka ruwa ya nufi gun Yesu.
30 Amma da ya ga iska ta yi ƙarfi sai ya ji tsoro. Da ya fara nutsewa sai ya yi kururuwa, ya ce, “Ya Ubangiji, ka cece ni!”