6 Sai Yesu ya ce musu, “Ku kula, ku yi hankali da yistin Farisiyawa da na Sadukiyawa.”
7 Sai suka yi magana da juna suka ce, “Ba mu kawo gurasa ba fa!”
8 Da Yesu ya lura da haka sai ya ce, “Ya ku masu ƙarancin bangaskiya, don me kuke magana da juna a kan ba ku zo da gurasa ba?
9 Ashe, har yanzu ba ku gane ba? Ba ku tuna da gurasa biyar ɗin nan na mutum dubu biyar ba? Kwando nawa kuka ɗauka?
10 Ko kuma gurasan nan bakwai na mutum dubu huɗu, manyan kwanduna nawa kuka ɗauka?
11 Yaya kuka kasa ganewa? Ba zancen gurasa na yi ba, sai dai ku yi hankali da yistin Farisiyawa da na Sadukiyawa.”
12 Sa'an nan ne fa suka fahimta cewa, ba ce musu ya yi, su yi hankali da yistin gurasa ba, sai dai su yi hankali da koyarwar Farisiyawa da ta Sadukiyawa.