15 Sai ya ɗora musu hannu ya yi tafiyarsa.
16 Sai ga wani ya matso wurinsa, ya ce, “Malam, wane aiki nagari ne da lalle zan yi in sami rai madawwami?”
17 Sai ya ce masa, “Don me kake tambayata a kan abin da yake nagari? Ai, Managarci ɗaya ne. In kuwa kana so ka sami wannan rai, to, ka kiyaye umarnan nan.”
18 Sai ya ce masa, “Waɗanne?” Yesu ya ce, “Kada ka yi kisankai. Kada ka yi zina. Kada ka yi sata. Kada ka yi shaidar zur.
19 Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, ka kuma ƙaunaci ɗan'uwanka kamar kanka.”
20 Saurayin ya ce masa, “Ai, duk na kiyaye waɗannan, me kuma ya rage mini?”
21 Yesu ya ce masa, “In kana so ka zama kammalalle, sai ka je ka sayar da duk mallakarka, ka bai wa gajiyayyu, ka sami wadata a Sama. Sa'an nan ka zo ka bi ni.”