24 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. In kun ba ni amsa, ni ma sai in gaya muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan.
25 To, baftismar da Yahaya ya yi, daga ina take? Daga Sama take, ko kuwa ta mutum ce?” Sai suka yi ta muhawwara da juna, suna cewa, “In muka ce, ‘Daga Sama take,’ sai ya ce mana, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’
26 In kuwa muka ce, ‘Ta mutum ce,’ ai, muna jin tsoron jama'a, don duk kowa ya ɗauki Yahaya a kan annabi ne.”
27 Sai suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Shi kuma ya ce musu, “Haka ni kuma ba zan faɗa muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan ba.”
28 “To, me kuka gani? An yi wani mutun mai 'ya'ya biyu maza. Ya je wurin na farkon, ya ce, ‘Ɗana, yau je ka ka yi aiki a garkar inabi.’
29 Sai ya ce, ‘Na ƙi.’ Amma daga baya sai ya tuba, ya tafi.
30 Sai ya je gun na biyun ya faɗa masa haka. Shi kuwa ya amsa ya ce, ‘To, za ni, baba,’ amma bai je ba.