31 Zai kuwa aiko mala'ikunsa su busa ƙaho mai tsananin ƙara, su kuma tattaro zaɓaɓɓunsa daga gabas da yamma, kudu da arewa, wato, daga wannan bangon duniya zuwa wancan.”
32 “Ku yi koyi da itacen ɓaure. Da zarar rassansa sun fara sakuwa, suna toho, kun san damuna ta yi kusa ke nan.
33 Haka kuma in kun ga duk waɗannan abubuwa, ku sani ya kusato, a bakin ƙofa ma yake.
34 Hakika, ina gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba sai duk abubuwan nan sun auku.
35 Sararin sama da kasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta shuɗe ba.”
36 “Amma fa wannan rana da wannan sa'a ba wanda ya sani, ko mala'ikun da yake Sama, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai.
37 Kamar yadda aka yi a zamanin Nuhu, haka dawowar Ɗan Mutum za ta zama.