58 Amma Bitrus ya bi shi daga nesa, har cikin gidan babban firist. Da ya shiga, sai ya zauna tare da dogaran Haikali, don ya ga ƙarshen abin.
59 To, sai manyan firistoci da 'yan majalisa duka suka nemi shaidar zur da za a yi wa Yesu don su sami dama su kashe shi.
60 Amma ba su samu ba, ko da yake masu shaidar zur da yawa sun zazzaburo. Daga baya sai waɗansu biyu suka matso,
61 suka ce, “Wannan ya ce, wai zai iya rushe Haikalin nan na Allah, ya kuma gina shi a cikin kwana uku.”
62 Sai babban firist ya miƙe ya ce, “Ba ka da wata amsa? Shaidar da mutanen nan suke yi a kanka fa?”
63 Amma Yesu na shiru. Sai babban firist ya ce masa, “Na gama ka da Allah Rayayye, ka faɗa mana ko kai ne Almasihu, Ɗan Allah.”
64 Sai Yesu ya ce masa, “Yadda ka faɗa. Ina kuwa gaya muku a nan gaba za ku ga Ɗan Mutum zaune a dama da Mai Iko, yana kuma zuwa a kan gajimare.”