11 Gama Nassi ya ce, “Duk mai gaskatawa da shi ba zai kunyata ba.”
12 Ai, ba wani bambanci a tsakanin Bayahude da Ba'al'umme. Ubangijin nan ɗaya shi ne Ubangijin kowa, mayalwacin baiwa ne kuma ga dukkan masu addu'a a gare shi.
13 “Duk wanda kuwa ya yi addu'a da sunan Ubangiji zai sami ceto.”
14 Amma ta ƙaƙa za su yi addu'a ga wanda ba su gaskata da shi ba? Ta ƙaƙa kuma za su gaskata da wanda ba su taɓa ji ba? Ta ƙaƙa kuma za su ji, in ba mai wa'azi?
15 Ta ƙaƙa kuma za su yi wa'azi, in ba aikarsu aka yi ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yaya zai kasance a isowar masu kawo bishara!”
16 Amma ba duka ne suka yi na'am da bisharar ba. Ishaya ma ya ce, “Ya Ubangiji, wa ya gaskata jawabinmu?”
17 Ashe, bangaskiya ta wurin jawabin da ake ji take samuwa, jawabin da ake ji kuma ta Maganar Almasihu yake.