2 Mun dai san hukuncin Allah a kan masu yin haka daidai ne.
3 Ya kai mutum, kai da kake ganin laifin masu yin haka, alhali kuwa kai kanka, kana yinsu, kana tsammani za ka tsere wa hukuncin Allah ne?
4 Ko kuwa kana raina yalwar alherinsa, da jimirinsa, da kuma haƙurinsa ne? Ashe, ba ka sani ba alherin Allah yana jawo ka zuwa ga tuba?
5 Amma ga shi, saboda ƙeƙasasshiyar zuciyarka marar tuba, kana nema wa kanka fushin Allah a ranar fushi, sa'ad da za a bayyana hukuncin Allah macancani.
6 Allah ne zai saka wa kowa gwargwadon aikinsa.
7 Waɗanda suke neman daraja da ɗaukaka da kuma dawwama ta wurin naciyarsu ga aikata nagarta, zai saka musu da rai madawwami.
8 Waɗanda suke masu sonkai, da waɗanda suke ƙin bin gaskiya, da masu bin rashin adalci, zai saka musu da fushi da hasala.