1 Sa'an nan na ga wani ƙaƙƙarfan mala'ika yana saukowa daga sama, lulluɓe da gajimare, da bakan gizo a bisa kansa, fuskarsa kamar rana, ƙafafunsa kuma kamar ginshiƙan wuta.
2 Ga wani ƙaramin littafi a buɗe a hannunsa. Sai ya tsai da ƙafarsa ta dama a kan teku, ƙafarsa ta hagu kuwa a kan ƙasa,
3 ya yi kira da murya mai ƙarfi, kamar zaki yana ruri. Da ya yi kiran, sai aradun nan bakwai suka yi tsawa.
4 Sa'ad da kuwa aradun nan bakwai suka yi tsawa, kamar zan rubuta, sai na ji wata murya daga sama tana cewa, “Rufe abin da aradun nan bakwai suka faɗa, kada ka rubuta.”
5 Sai mala'ikan nan da na gani a tsaye a teku da ƙasa ya ɗaga hannunsa na dama sama,