1 Sa'an nan na duba, sai ga Ɗan Ragon nan a tsaye a kan Dutsen Sihiyona, akwai kuma mutum dubu ɗari da dubu arba'in da huɗu tare da shi, waɗanda aka rubuta sunansa, da sunan Ubansa, a goshinsu.
2 Sai na ji wata murya daga Sama kamar ƙugin ruwa mai gudu, kamar aradu mai ƙara, muryar da na ji kuwa, kamar ta masu molo ce na kiɗan molo.
3 Suna raira wata sabuwar waƙa a gaban kursiyin, a gaban rayayyun halittan nan huɗu, da kuma a gaban dattawan nan. Ba mai iya koyon waƙar nan, sai mutum dubu ɗari da dubu arba'in da huɗu ɗin nan, waɗanda aka fanso daga duniya.
4 Waɗannan su ne waɗanda ba su taɓa ƙazantuwa da fasikanci ba, domin su tsarkaka ne. Su ne kuma suke bin Ɗan Ragon a duk inda ya je. Su ne kuma aka fanso daga cikin mutane a kan su ne nunan fari na Allah, da na Ɗan Ragon nan kuma,