16 Sai wanda yake a zaune a kan gajimaren ya wurga laujensa zuwa duniya, aka girbe amfanin duniya.
17 Wani mala'ika kuma ya fito daga Haikali a Sama, shi ma kuwa yana da kakkaifan lauje.
18 Sai kuma wani mala'ika ya fito daga bagadin ƙona turare, wato, mala'ikan da yake da iko da wutar, ya yi magana da murya mai ƙarfi da wannan mai kakkaifan lauje, ya ce, “Ka sa laujenka ka yanke nonnan inabin zuwa duniya, don inabin ya nuna.”
19 Sai mala'ikan ya wurga laujensa duniya, ya tattara inabin duniya, ya zuba a cikin babbar mamatsar inabi ta fushin Allah.
20 Aka tattake mamatsar inabin a bayan gari, jini kuma ya yi ta gudana daga mamatsar inabin, ya kai kamar tsawon linzami a bakin doki, har mil metan.