5 Bayan wannan na duba, ga Wuri Mafi Tsarki a buɗe a Haikali a Sama.
6 Sai mala'ika bakwai ɗin nan masu bala'i bakwai suka fito daga Haikalin, saye da tufafin lilin mai tsabta, mai ɗaukar iko, da ɗamarar zinariya a ƙirjinsu.
7 Sai ɗaya daga cikin rayayyun halittan nan guda huɗu, ta ba mala'ikun nan bakwai tasoshi bakwai na zinariya, a cike da fushin Allah, shi da yake a raye har abada abadin.
8 Sai Haikalin ya cika da hayaƙi mai fitowa daga ɗaukakar Allah da ikonsa. Ba mai iya shiga Haikalin nan, sai bayan bala'i bakwai na mala'ikun nan bakwai sun ƙare.