1 Bayan haka, na ga wani mala'ika yana saukowa daga Sama, mai iko da yawa, sai aka haskaka duniya da ɗaukakarsa.
2 Sai ya yi kira da murya mai ƙarfi, ya ce,“Ta fāɗi! Babila mai girma ta fāɗi!Ta zama mazaunin aljannu,Matattarar kowane baƙin aljani,Da kowane irin ƙazamin tsuntsu, abin ƙyama.
3 Dukkan al'ummai sun yi tsananin jarabar yin fasikanci da ita,Sarakunan duniya kuma sun yi fasikanci da ita,Attajiran duniya kuma sun arzuta da almubazzarancinta.”
4 Sai na ji wata murya daga Sama, tana cewa,“Ku fito daga cikinta, ya ku jama'ata,Kada zunubanta su shafe ku,Kada bala'inta ya taɓa ku.