13 da kirfa, da kayan yaji, da turaren wuta, da mur, da lubban, da ruwan inabi, da mai, da garin alkama, da alkama, da shanu, da tumaki, da dawaki, da kekunan doki, da kuma bayi, wato, rayukan 'yan adam.
14 “Amfanin da kika ƙwallafa rai a kai, har ya kuɓuce miki,Kayan annashuwarki da na adonki sun ɓace miki, ba kuwa za a ƙara samunsu ba har abada!”
15 Attajiran waɗannan hajjoji da suka arzuta a game da ita, za su tsaya a can nesa don tsoron azabarta, suna kuka, suna baƙin ciki, suna cewa,
16 “Kaito! Kaiton babban birnin nan!Wanda dā ya sa lallausan lilin, da tufafi masu ruwan jar garura, da kuma jan alharini,Wanda ya ci ado da kayan zinariya, da duwatsun alfarma, da lu'ulu'u!
17 Domin a sa'a ɗaya duk ɗumbun dukiyar nan ta hallaka.”Sai duk masu jiragen ruwa, da masu shiga, da masu tuƙi, da duk waɗanda cinikinsu ya gamu da bahar, suka tsaya a can nesa,
18 suna kururuwa da suka ga hayaƙin ƙunarsa, suna cewa,“Wane birni ne ya yi kama da babban birnin nan?”
19 Har suka tula wa kansu ƙasa suna ta kuka, suna baƙin ciki, suna kururuwa, suna cewa,“Kaito! Kaiton babban birnin nan!Wanda duk masu jiragen ruwa a bahar suka arzuta da ɗumbun dukiyarsa,A sa'a ɗaya ya hallaka.