18 ku ci naman sarakuna, da naman sarakunan yaƙi, da naman ƙarfafa, da naman dawakai, da na mahayansu, da naman kowa da kowa, wato, na ɗa da na bawa, na yaro da na babba.”
19 Sai na ga dabbar nan, da sarakunan duniya, da rundunoninsu, sun taru, don su yaƙi wanda yake kan dokin, da kuma rundunarsa.
20 Sai aka kama dabbar, da kuma annabin nan na ƙarya tare da ita, wanda ya yi al'ajabai a gabanta, waɗanda da su ne ya yaudari waɗanda suka yarda a yi musu alamar dabbar nan, da kuma waɗanda suka yi wa siffarta sujada. Waɗannan biyu kuwa aka jefa su da ransu a cikin tafkin wuta da ƙibiritu.
21 Sauran kuwa aka sare su da takobin wanda yake a kan doki, wato, da takobin nan da yake fitowa daga cikin bakinsa. Dukan tsuntsaye kuwa suka ci namansu har suka yi gamba.