3 Sai suka sāke yin sowa, suna cewa,“Halleluya! Hayaƙinta yana tashi har abada abadin.”
4 Sai dattawan nan ashirin da huɗu, da rayayyun halittan nan huɗu, suka fāɗi suka yi wa Allah sujada, shi da yake zaune a kan kursiyin, suna cewa, “Amin. Halleluya!”
5 Sai aka ji wata murya daga kursiyin, tana cewa,“Ku yabi Allahnmu, ya ku bayinsa,Ku da kuke jin tsoronsa, yaro da babba.”
6 Sai na ji kamar wata sowar ƙasaitaccen taro, kamar ƙugin ruwa mai gudu, kamar aradu mai ƙara, suna cewa,“Halleluya! Gama Ubangiji AllahnmuMaɗaukaki shi ne yake mulki.
7 Mu yi ta murna da farin ciki matuƙa,Mu kuma ɗaukaka shi,Domin bikin Ɗan Ragon nan ya zo,Amaryarsa kuma ta kintsa.
8 An yardar mata ta sa tufafin lallausan lilinmai ɗaukar ido, mai tsabta.”Lallausan lilin ɗin nan, shi ne aikin adalci na tsarkaka.
9 Sai mala'ikan ya ce mini, “Rubuta wannan, ‘Albarka tā tabbata ga waɗanda aka gayyata, zuwa cin abincin bikin Ɗan Ragon nan.’ ” Ya kuma ce mini, “Wannan ita ce Maganar Allah ta gaskiya.”