11 yana tare da ɗaukakar Allah. Hasken birnin yana ƙyalƙyali kamar wani irin nadirin dutse mai daraja, kamar yasfa, garau kamar ƙarau.
12 Yana da babban garu mai tsawo, da ƙofar gari goma sha biyu, a ƙofofi ɗin da akwai mala'iku goma sha biyu. A jikin ƙofofin kuma an rubuta sunayen kabilan nan goma sha biyu na Isra'ila,
13 a gabas, ƙofa uku, a yamma ƙofa uku, a kudu ƙofa uku, a arewa kuma ƙofa uku.
14 Garun birnin kuwa, tana da dutsen harsashi goma sha biyu, a jikinsu kuma an rubuta sunayen manzannin nan goma sha biyu na Ɗan Ragon.
15 Shi wanda ya yi mini magana kuwa yana da sandar awo ta zinariya, domin ya auna birnin, da ƙofofinsa, da garunsa.
16 Birnin murabba'i ne, tsawonsa da fāɗinsa duka ɗaya ne. Sai ya auna birnin da sandarsa, mil dubu da ɗari biyar, tsawonsa, da fāɗinsa da zacinsa, duka ɗaya suke.
17 Ya kuma auna garunsa, kamu ɗari da arba'in da huɗu ne na mutum, wato, na mala'ika ke nan.